Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Salah na cikin 'yan wasan Afrika 30 da ke tseren lashe gwarzon shekara

Muhammad Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool na cikin sahun ‘yan wasan Afrika 30 da suka shiga tseren lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrikan ta bana.

Muhammad Salah na Masar yayin karbar kyautar gwarzon shekara na Afrika a bara.
Muhammad Salah na Masar yayin karbar kyautar gwarzon shekara na Afrika a bara. CRISTINA ALDEHUELA / AFP
Talla

Sai dai a wannan karon ana ganin Salah wanda shi ke rike da kambun na gwarzon dan wasan Afrika, ka iya rasawa musamman ganin irin rawar da takwaransa na Senegal Sadio Mane ke takawa a bangaren kasarsa da kuma Liverpool baki daya.

Ana dai ganin Mane ka iya buge Salah sakamakon yadda Masar ta yi rashin katabus a gasar cin kofin Afrika a bangare guda shi kuma Mane ya kai har ga wasan karshe na gasar a bana.

Matukar dai Salah ya sake lashe kyautar a bana zai zamo kenan karo na 3 a jere da matashin dan wasan ke doke zakakuran ‘yan kwallon nahiyar ta Afrika.

Cikin ‘yan wasan na Afrika da suka shiga tseren lashe kyautar baya ga Salah Mane da kuma Naby Keita daga Liverpool akwai ‘yan wasan Arsenal Aubameyang da Nicolas Pepe kana Jordan Ayew da Wilfried Zaha daga Crystal Palace sannan Riyad Mahrez na Manchester City da kuma Wilfred Ndidi daga Leicester City kana Mahmoud 'Trezeguet' Hassan na Aston Villa dukkaninsu masu doka Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.