Haramta cinikin jakuna a Duniya
Matsalar kashe jakuna ta zama babbar barazana ga yawan jakuna da ake dasu a Duniya inda masana ke cewa idan ba’a dauki matakin da ya dace ba, ana iya rasa kusan rabi na jakunan nan da shekaru 5. Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da Najeriya ke shirin yin doka kan haramta kashe jakuna, yayin da kungiya mai suna Donkey Sanctuary ta kaddamar da rahoto kan hakan a Abuja dake Najeriya.
A cikin shirin Bashir Ibrahim Idris ya duba irin matsalolin da ake fuskanta a wasu yankunan kasashen Afrika.