Isa ga babban shafi

CPJ ta karrama wasu jajirtattun 'yan jaridu

Kungiyar da ke kare hakkin ‘yan jarida ta Duniya CPJ, a daren Alhamis ta karrama ‘yan jaridu daga Brazil da India da Nicaragua, da kuma Tanzania a birnin New York na Amurka, bikin karrama ‘yan jaridun karo na 29, da kungiyar ta baiwa shahararren dan jaridan kasar Pakistan Zaffar Abbas kyautar Gwen Ifill.

Logon kungiyar kare hakkin 'yan jaridu ta Duniya CPJ
Logon kungiyar kare hakkin 'yan jaridu ta Duniya CPJ DS
Talla

Dukkannin wadanda aka karrama suna aiki ne a kasashe masu tasowa, inda dimokaradiyya ba ta yi karfi ba.

Jajirtattun ‘yan jarida ne da suka fuskanci muzgunawa a yankunan su, kuma suka yi tsayuwar gwamin - jaki wajen gudanar da ayyukan su duk da sa ido da barazana daga hukumomi.

Tun da farko a wannan makon, wadanda aka karraman, sun gana da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence don bayyana takaicin su kan barazanar da yancin ‘yan jarida ke fuskanta, da kuma batun labaran kanzon kurege da shugabannin kasashen su ke yawan daukowa.

An mika kyautuka ga ‘yan jarida da dama da suka shiga tsanani wajen gudanar da ayyukan su, ciki har da Lucia Pineda Ubau da Miguel Mora da aka sake su a ranar 11 ga watan Yuni bayan sun shafe watanni 6 a gidan kaso a Nicaragua.

A wani yanayi mai sosa zuciya, illahirin wadanda suka taru a dakin taron sun mike tsaye yayin da aka gabatar da ‘yan jaridan Reuters Wa Lone da Kyaw Soe Oo da suka shafe kwanaki dari 5 a gidan yari yayin da suke aiki a Myanmar.

Cikin wadanda aka karrama harda wani shaharerren dan jaridar kasar Tanzania Maxence Melo Mubyazi, wanda ya yi kaurin suna a Gabashi da kuma Tsakiyar kasar wajen fallasa gazawar gwamnati akasari da harshen Kiswahili a jaridar sa dake kafar Intanet.

A shekarar 2016, jami’an tsaron Tanzania sun mamaye ofishin sa, inda suka tsare Melon a dan lokaci don yi masa tambayoyi bisa zargin aikata laifuka ta kafar intanet, kafin daga bisani aka sauya laifin zuwa tafiyar da harkokin sa ba tarer da rajista ba, da kuma rashin fallasa masu sauraren sa a kafar sadarwar sa.

Abokin aikinmu a sashen Hausa na RFI, Ahmed Abba ya taba karbar wannan kyauta sakamakon garkame shi da gwamnatin Kamaru ta yi yayin gudanar da aikinsa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.