Isa ga babban shafi
Afrika

Harin Ta'addanci ya jefa Sahel cikin kunci

Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace tashin hankalin da Yan ta’adda keyi a Yankin Sahel ya tilastawa mutane akalla milyan guda tserewa daga gidajen su a kasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, matsalar da ta shafi aikin noma da kuma bukatar agaji.

Yankin Sahel
Yankin Sahel RFI/Sayouba Traoré
Talla

Mai Magana da yawun kungiyar, Herve Verhoosel yace duniya ta gaza wajen fahimtar illar da tashin hankali ya yiwa Yankin sahel, kuma rashin daukar matakan da suka dace cikin gaggawa na iya jefa milyoyin mutane cikin hadari.

Hukumar tace mutane sama da 860,000 suka rasa matsugunan su a kasashen 3, yayin da kusan miliyan biyu da rabi kuma na bukatar agajin abinci cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.