Isa ga babban shafi
Faransa-Afrika

Faransa za ta mayar wa Afrika kayayyakin tarihin ta

Firaministan Faransa Edourad Philippe ya jaddada aniyar shugaba Emmanuel Macron na mayar wa nahiyar Afirka kayayyakin tarihin ta da aka jibge a Paris na kasar ta Faransa.

Édouard Philippe tareda Shugaban kasarSenegal  Macky Sall a Dakar
Édouard Philippe tareda Shugaban kasarSenegal Macky Sall a Dakar RFI/Charlotte Idrac
Talla

Firaministan Faransa Edouard Phillipe tareda rakiyar ministocin Faransa guda shida suna kasar Sanegal a yau lahadi, ziyarar da zasu yi amfani da ita domin yin bitar dama kare daddadiyar huldar dake tsakanin Faransa da Sanegal.

Yayin ziyarar aikin da ya fara a Dakar, Philippe da shugaba Macky Sall sun sanya hannu akan yarjeniyoyi da dama da suka hada da na al’adu.

Kasar Faransa na da kayayyakin tarihin da aka kai daga Afirka da suka kai akalla 90,000, yayin da shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin mayar da su kasashen da suka fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.