Isa ga babban shafi
Mali

Sojojin Mali sun zakulo gawarwaki 20 daga rijiya

Akalla mutane dubu 15 ne suka gudanar da gangamin nuna goyon baya ga sojojin kasar Mali a birnin Bamako.

Wasu daga cikin dakarun kasar Mali.
Wasu daga cikin dakarun kasar Mali. AFP/Michele CATTANI
Talla

Tattakin dubban jama’ar ya gudana ne, jim kadan bayan gano gawarwakin mutane akalla 20 da aka zuba cikin wata rijiya da dakarun na Mali suka yi a kauyen Peh, na yankin Mopti dake tsakiyar kasar.

Sanarwar da gwamnatin Mali ta fitar a wannan Juma’a ta ce an aike da sojojin kauyen na Peh ne, bayan samun rahoton cewa wasu mahara sanye da kayan mafarauta sun kaiwa kayuen farmaki inda suka halaka mutane da dama gami da in awon gaba da dabbobi.

A baya bayan nan, yankin Mopti dake tsakiya Mali yayi kaurin suna wajen fuskantar tashe-tashen hankula masu alaka da fadan kabilanci da kuma hare-haren mayaka masu ikirarin Jihadi.

Akalla sojojin Mali 100 mayakan masu ikirarin jihadi suka halaka a 'yan makwannin da suka gabata, yayin hare-haren da suka kaddamar kan sansanonin sojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.