Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Shugaban Congo ya sha alwashin kawar da Ebola a 2019

Shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi ya sha alwashin kawar da cutar Ebola daga kasar a karshen wannan shekara.

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo Félix Tshisekedi.
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo Félix Tshisekedi. Sumy Sadurni / AFP
Talla

Alwashin da shugaban ya sha yayin ziyarar da ya kai Jamus, na zuwa ne bayan da aka kaddamar da sabbin magungunan cutar ta Ebola har kashi biyu.

Cikin watan Agustan shekarar bara, annobar ta sake bulla a lardin arewacin Kivu dake Jamhuriyar Congo, daga bisani ta yadu zuwa kudancin lardin na Kivu da kuma Ituri, wadanda ke iyaka da kasashen Uganda, Rwanda da kuma Burundi.

Tun bayan sake bullar tata zuwa wannan lokaci, annobar ta halaka sama da mutane dubu 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.