Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 11/12 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 11/12 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 11/12 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 11/12 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 11/12 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 11/12 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 11/12 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 08/12 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 11/12 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 08/12 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 11/12 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

GUTA za ta durkusar da harkokin 'yan Najeriya a Ghana

media Wasu daga cikin mambobin kungiyar kwadago ta Ghana Daily Trust

Kungiyar Kwadagon Ghana GUTA na shirin gudanar da gagarumin aikin rufe shagunan ‘yan Najeriya da ke birnin Accra, matakin da ake kallo a matsayin ramuwar gayya kan rufe iyakokin Najeriya.

Kawo yanzu Kungiyar Kwadagon ta GUTA ta rufe shagunan ‘yan Najeriya kimanin 70 da zummar durkusar da harkokin kasuwancin ‘yan Najeriyar a birnin Accra.

Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya da ke Ghana, Chukwuemeka Nnaji ya bukaci mambobin kungiyar da su rufe shagunansu domin kauce wa fashe-fashe ko kuma lalata musu kayayyakinsu na sana’a.

Kiris ya rage a yi mummunar arangama tsakanin ‘yan Ghana da ‘yan Najeriya a jiya a birnin na Accra saboda yadda kungiyar kwadagon ke ci gaba da rufe shagunan.

Matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na rufe kan iyakokinta da kasashe makwabta da suka hada da Ghana, ya jefa harkokin ‘yan kasuwan na Ghana cikin wani hali.

Najeriya ta jaddada cewa, ba za ta bude kan iyakarta a yanzu.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure