Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan Boko Haram na rike da wasu kananan hukumomi biyu a Najeriya

Wasu rahotanni daga kungiyoyin dake sa ido dangane da batutuwa da suka jibanci ayukan jinkai a Najeriya sun gano cewa akalla mutane milyan 1 da dubu 200 ne Boko Haram suka yi wa kafar-rago, a cikin kananan hukumomi biyu a Jihar Barno.

Wasu daga cikin yankunan dake karkashin kungiyar Boko Haram a jihar Borno
Wasu daga cikin yankunan dake karkashin kungiyar Boko Haram a jihar Borno Fati Abubakar/RFI
Talla

Al’umomin yankunan da lamarin ya shafa ,na cikin wani halin rashin tabbas dangane da batun tsaro, hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da hukumomin kasar ke ci gaba da bayyana cewa suna daf da kawo karshen kungiyar Boko Haram. Banda haka a dan tsakanin nan yan kungiyar ta Boko Haram sun kai wasu jerryn hare-hare tareda kisan sojojin Najeriya.

To domin ji yadda masana ke kallon rahoton Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Khalifa Dikwa, masanin tsaro a najeriya, ga kuma yadda hirarsu ta kaya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.