Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda za ta fara fitar da danyen mai

Nan ba da jimawa ba Uganda za ta bi sawun kasashen da ke fitar da danyen man fetur, inda ake sa ran ta fitar da shi a karon farko daga tekun Albert zuwa kasuwannin kasashen waje.

Shugaban Ugandan  Yuweri Museveni.
Shugaban Ugandan Yuweri Museveni. Ug.gov
Talla

Wannan ya biyo bayan yarjejeiyar da Ugandan ta cimma da Tanzania ne, wacce ta ba ta damar amfani da bututun mai na gabashin Afrika wajen fitar da danyen man ta zuwa kasashen waje.

Ministar makamashin kasar, Irene Margaret Muloni ta ce lokaci ne na farin ciki, ganin cewa kasar ta dau tsawon lokaci kafin ta kawo inda take a wannan aiki na samar da danyen mai.

Ta ce an gano gangan danyen mai biliyan shida a aikin da aka yi na neman albarkatun, kuma kasar tana da shirin hako ganga biliyan 1 da miliyan dari 4 daga cikinsu.

Kasar tana shirin gina matatar mai a Kabaale, gundumar Hoima dake yammacin Uganda, a gabashin gabar tekun Albert kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Dimokaradiyyar congo, wacce ake sa ran kammalawa a shekarar 2022.

Duk da wannan ci gaba, Uganda tana sa ido kan sauran albarkatu da Allah ya albarkace ta da su bayan ta fara bayar da lasisin hakar mai ga wasu kamfanoni da ke cikin harkar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.