Isa ga babban shafi
Najeriya-Rasha

Sabon babin zumunci ya bude tsakanin Najeriya da Rasha- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce karkashin sabuwar alaka tsakanin kasar da Rasha, sabbin makamashi za su shiga Najeriyar bisa alkawurran da za su fadada tsohuwar dangantar kasashen biyu ta fuskar kimiyya kasuwanci da kuma makamashi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwarinsa na Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwarinsa na Rasha Vladimir Putin. Pulse.ng
Talla

Cikin wata sanarwar gwamnatin Najeriya bayan taron da shugabannin Afrika fiye da 40 ke halarta a Rasha, ta ruwaito Muhammadu Buhari na cewa taron zai farfado da alakar kasar da tsohuwar tarayyar Soviet.

Muhammadu Buhari na Najeriyar, ya ce bisa yarjejeniyar da suka kulla da Rasha bangarorin biyu za su yi cudanya tare da amfanar da juna ta fuskar Cinikayya Kimiyya al’adu da kuma ilimi.

Taron na kasashen Nahiyar Afrika da Rasha irinsa na farko karkashin jagorancin shugaba Vladimir Putin, Muhammadu Buhari ya ce Rasha tsohuwar abokiyar Najeriya ce tun a lokacin yakin basasa ta yadda ta tallafa matuka wajen tabbatar da wanzuwar Najeriya kasa guda dunkulalliya.

A shekarun 1960 dai Rashan ta taimaka a Najeriya ta bangarorin da suka shafi Ilimi albarkatun karkashin kasa da tsaro baya taiamakwa wajen bunkasa kasar.

Sai dai a wannan karon Muhammadu Buhari ya ce alakar Najeriya da Rasha za ta fi mayar da hankali wajen bunkasa albarkatun man fetur da gas da kuma taimakon Soji musamman a yaki da Boko Haram.

Cikin kalaman Muhammadu Buhari ya ce abin farin ciki sake dawowar alakar ta Najeriya da Rasha wadda su ke fatan kowanne bangare ya amfana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.