Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 18/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 18/11 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 18/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 18/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 15/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 14/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 15/11 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 15/11 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 15/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Putin zai karbi bakuncin shugabannin Afrika 45 a Rasha

media Shugaban Rasha Vladimir Putin Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS

Shugaban Rasha Vladmir Putin na shirin karbar bakwancin shugabannin kasashen Africa, a wani taron karfafa dankon zumunci tsakanin Nahiyar da Moscow irinsa na farko a tarihi, taron da ake sa ran Rashan ta alkawarta taimakawa kasashen ta hanyar basu gudunmawa ba tare da gindaya sharudda kwatankwacin na kasashen yammaci ba.

Sanarwar da fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta fitar ta ce akalla shugabannin kasashen Africa 47 ake dakon isarsu garin Sochi wajen da taron zai gudana wanda za a fara tsakanin ranakun gobe Laraba da jibi Alhamis.

Tuni dai Rashan ta bayyana alfahari da yadda kasashen na Afrika suka amsa goron gayyatarta zuwa taron wanda ke da nufin karfafa dankon zumunci tsakanin kasar da nahiyar ta fuskar kasuwanci, siyasa, tsaro da kuma bunkasa ci gaba.

Africa wadda ke da kasashe 54 a hukumance ana ganin za ta ci moriyar alakar da Rasha wadda ke matsayin kasa mafi noma da kuma fitar da alkama a duniya baki daya baya ga kaurin sunanta ta fuskar samar da makamai.

A bangare guda itama Rashan alakar za ta bunkasa kasuwancinta musamman ta fuskar takin zamaninta dai dai lokacin da manyan kasashen Afrikan ke kokarin karkata kasuwancinsu zuwa fannin noma.

Kawo yanzu dai Amurka ta bayyana matakin na Rasha a wani sabon salon mamaye harkokin kasuwanci a nahiyar ta Afrika kwatankwacin zargin da Amurkan ke yi ga Rasha, inda Washington ta sha alwashin bayar da kariya ga Afrikan don hana mamayar Rasha da China.

Sai dai tuni shugaban Rasha Vladimir Putin ya soki matakin yin rige-rigen kulla zumunta da wasu manyan kasashen duniya ke yi da nahiyar ta Africa inda yake gargadin haka.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure