Isa ga babban shafi
Mali

Sojin Mali sun halaka 'yan bindiga 50 tare da kubutar da jami'ansu

Rundunar Sojin Mali ta sanar da kashe 'yan bindiga kusan 50 da kuma kubutar da sojojin da akayi garkuwa da su, bayan wani kazamin harin da aka kai sansanonin su guda biyu a watan jiya.

Wasu dakarun sojin Mali
Wasu dakarun sojin Mali REUTERS/Feisal Omar
Talla

Sanarwar da rundunar sojin Mali ta gabatar ya nuna cewar ta yi nasarar kashe 'yan bindigar kusan 50 da jikkata wasu 30, tare da lalata makaman su, a wani samame da suka kai musu.

Rundunar sojin ta ce ta kuma kubutar da sojojin ta 36 daga cikin kusan 60 da suka bata, sakamakon harin 'yan bindigar a watan Satumba, wanda ya sa iyalan su gudanar da zanga zanga domin sanin halin da suke ciki.

Yayin harin na watan Satumba, Yan bindigar sun kashe sojojin Mali 38, a hari mafi muni da aka taba gani, tun bayan tashin hankalin da ya barke a kasar a shekarar 2012, lokacin da Yan bindigar suka kwace boren da Abzinawa suka yi.

Wannan ya sa Faransa girke dakaru 12,000 da kuma jagorancin kafa rundunar G5 Sahel wadad ta samu sojoji daga kasashen Mauritania da Mali da Nijar da Chadi da kuma Burkina Faso domin magance hare haren su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.