Isa ga babban shafi
Guinea

Guinea ta gurfanar da Jagororin adawa 8 gaban Kotu kan zanga-zanga

Gwamnatin Guinea ta gurfanar da wasu jagororin ‘yan adawa 8 gaban kotu, wadanda ake zargi da kitsa zanga-zangar adawa da matakin shugaba Alpha Conde na yunkurin sake tsayawa neman kujerar shugabancin kasar a karo na 3.

Shugaban kasar Guinea Alpha Condé
Shugaban kasar Guinea Alpha Condé ©FREDERICK FLORIN/AFP
Talla

Tun bayan matakin Shugaba Alpha Conde mai shekaru 81, na sake tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar a karo na 3, jagororin ‘yan adawa suka bukaci kalubalantarsa inda ake zarginsu da ingiza jama’ar kasar.

Kusan wata guda kenan al’umma na zanga-zanga kan matakin na Alpha Conde bayan da shugaban ya tirsasa zartas da wani kuduri karkashin kundin tsarin mulkin kasar da ya sahale masa sake tsayawa takarar a hukumance.

Mutanen 8 wadanda yanzu haka aka gurfanar da su gaban kotu, sun kunshi jagororin babbar jam’iyyar adawa baya ga na kungiyoyin fararen hula, inda gwamnati ke zarginsu da haddasa yamutsun da yak ai ga kisan jama’a baya ga bannata kayaki.

Masu shigar da kara na neman kotun ta yankewa mutanen hukuncin daurin shekaru akalla 3 zuwa 5 a gidan yari, sai dai lauyan da ke kare ‘yan adawar Salifou Beavogui ya bayyana cewa basu aikata laifin da za a yanke musu hukunci ba, hasalima jami’an gwamnati ne suka yi amfani da karfi kan dandazon masu zanga-zangar.

Akalla mutane 6 aka tabbatar da mutuwarsu yayinda wasu da dama kuma suka jikkata bayan barkewar zanga-zangar a Conakry kasar da ke fuskantar matsanancin talauci tun bayan hawa mulkin Conde a shekarar 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.