A yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don tattaunawa da duba matsalolin dake addabar matan karkara a fadin duniya.Taken ranar ta yau dai itace ''gina mata don samun yanayi mai kyau na rayuwa.''Goshin laasar jiya Litinin wakilinmu dake Sokoto ya shiga karkaran jihar Sokoto ya lalubo wata mace, talaka, da ke kauye wadda cimaka ke mata wuya, ko kuma wadda tun wayewar gari har goshin laasar bata karya kumallo ba.Ilai kuwa Faruk Yabo yayi katarin samun wannan baiwar Allah.
Talla
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu