Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Yan gudun hijira dubu 267 suka tsere daga gidajen su

A jiya juma’a, hukumar yan gudun hijar ta fitar da wasu alkaluma, inda ta nuna cewa akala mutane dubu 267 ne suka tsere daga matsugunin su a arewacin Burkina Faso sanadiyar hare-hare.

Rock Marc Chrisitan Kaboré  Shugaban kasar Burkina Faso
Rock Marc Chrisitan Kaboré Shugaban kasar Burkina Faso Johannes EISELE / AFP
Talla

Wasu alkaluma daga ita hukumar na nuni cewa wasu mutane dubu 486.000 ne suka samu mafaka a cikin wasu biranai na kasar ta Burkina Faso a cewar Andrew Mbogori shugaban hukumar yan gudun hijira ta Majalisar Dimkin Duniya.

Jami’in ya ce ba shida tabbaci yiyuwar dawowar wadanan mutane zuwa yankunan su ko gidajen su nan gaba.

Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore na ci gaba da yin kira zuwa Shugabanin kasashen Sahel don magance lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.