Isa ga babban shafi

Kotun Najeriyar ta ki ba da belin mawallafin Cross Rivers Watch

Wata kotu a Calabar da ke Najeriya ta ki amincewa da bukatar bayar da belin mawallafin Jaridar ‘Cross River Watch’ Austin Jalingo da aka kama kusan watanni biyu da suka gabata saboda zargin da ake masa na wallafa wani rahoto da ya soki Gwamnan Jihar Ben Ayade.

Mawallafin jaridar Cross Rivers Watch
Mawallafin jaridar Cross Rivers Watch RFI Hausa
Talla

Bayan kwashe sama da wata guda a hannun jami’an tsaro, an gurfanar da Jalingo a gaban wata kotun tarayya da ke Calabar ranar 25 ga watan Satumba, inda aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa da kuma yunkurin kifar da gwamnatin Jihar.

Lauyan sa ya bukaci kotu ta bayar da belinsa amma a hukuncin sa na yau, alkalin kotun Simon Amobeda ya ki amincewa da bukatar, inda ya bayar da umurnin cigaba da tsare Jalingo a gidan yari.

A watan jiya, kungiyar da ke kare hakkokin 'yan Jaridu ta duniya, CPJ ta bukaci gaggauta sakin mawallafin wanda ta ce yana gudanar da aikin sa bisa ka’ida amma kuma har ya zuwa yanzu babu abinda ya sauya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.