Isa ga babban shafi
Mali

'Yan tawaye sun kashe sojojin Mali 25

Gwamnatin kasar Mali ta ce, 'yan tawaye masu dauke da makamai sun kashe mata akalla sojoji 25 sakamakon kazamin harin da suka kai sansanonin sojin da ke tsakiyar kasar, yayin da wasu 60 suka bace.

Wasu daga cikin sojojin Mali
Wasu daga cikin sojojin Mali Sebastien RIEUSSEC / AFP
Talla

Kashe wannan adadi na sojojin Mali shi ne mafi muni da aka gani na baya-bayan nan sakamakon hare-haren da sojojin ke fuskanta daga kungiyoyin 'yan ta’addan da ke da alaka da Al-Qaeda ko kuma IS wadanda ke ci gaba da zama babbar barazana ga yankin Sahel baki daya.

Hukumomin kasar sun sanar da cewar, ana kai hare-haren ne a sansanonin sojin da ke Boulkessi da Mondoro, abin da ya yi sanadiyar kashe sojojin 25 da kuma bacewar akalla 60 tare da manyan makamai.

Sanarwar ta ce, dakarun gwamnatin kasar sun kaddamar da wani harin hadin gwuiwa tare da takwarorinsu na Burkina Faso da kuma taimakon sojin Faransa da ke yankin domin samo sojin da suka bata da kuma korar maharani daga yankin, abin da ya kai ga kashe 15 daga cikin su.

Arewacin Mali ya fada cikin tashin hankali tun bayan shekarar 2012 da 'yan tawaye suka mamaye yankin, kafin sojin Faransa su kore su.

Mayakan da ke dauke da makamai a yankin sun yi sanadiyar rasa dimbin rayuka a Mali da Nijar da Burkina Faso, abin da ya sa aka kafa rundunar G5 Sahel domin yaki da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.