Isa ga babban shafi
Bangladesh

'Yan Bangladeshi fiye da 400 aka kashe a Afrika ta kudu- Gwamnati

Gwamnatin Bangladash ta ce 'yan kasar sama da 400 aka kashe a Afirka ta kudu, a cikin shekaru 4 da suka gabata, sakamakon hare haren da ake kai wa baki 'yan kasashen waje.

Sheikh Hasina Wazed Firaministar Bangladesh
Sheikh Hasina Wazed Firaministar Bangladesh Reuters
Talla

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da mayar da hankali kan hare haren da ake kai wa baki 'yan kasashen waje a Afirka ta kudu, gwamnatin Bangladesh ta fitar da alkaluman da ke nuna cewar, 'yan kasar ta 452 aka kashe daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Jakadan Bangladesh a Afirka ta kudu, Shabbir Ahmad Chowdhry ya ce a cikin wannan shekara kadai 'yan kasar 88 aka kwashi gawar su zuwa gida, yayin da ake birne wasu ba tare da an shaidawa ofishin sa ba.

Chowdhry ya ce akasarin wadanda aka kashe, an hallaka su ne ta hanyar harbi da bindiga a shagunan su ko kuma kisan gilla sakamakon rikicin kasuwanci ko rigima kan kudade ko kuma alaka da mata.

Ganin yadda aikata laifuffuka ya yi kamari a Afirka ta kudu, jami’in ya ce wasu 'yan kasar sa kan yi hayar 'yan bindiga su hallaka abokan rikicin su.

Abdul Awal Tansen, daya daag cikin shugabannin 'yan Bangladesh mazauna kasar ya ce akwai mutanen su da dama da aka kashe ba tare da sun kai kara ba, saboda ba su da takardun zama.

'Yan kasar Bangladesh sun fara hijira zuwa Afirka ta kudu ne a shekara ta 2000, kuma yanzu haka adadin su ya kai 300,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.