Isa ga babban shafi

An gaza hukunta makasan masu zanga-zanga 150 a Guinea- MDD

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majlisar Dinkin Duniya ta bukaci bin kadi tare da daukar mataki kan wadanda ke da hannu a kisan masu zanga-zangar adawa fiye da 150 shekaru 10 da suka gabata a kasar Guinea.

Michelle Bachelet babbar jami'ar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya
Michelle Bachelet babbar jami'ar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya CRISTIAN HERNANDEZ / AFP
Talla

Cikin sanarwar babbar jami’ar hukumar Michelle Bachelet ta ce shari’ar na tafiyar hawainiya ta yadda aka gaza biwa mutanen hakkinsu, ciki har da mata fiye da dari da aka yiwa Fyade yayin zanga-zangar.

A ranar 28 ga watan Satumban 2009 ne Jami’an tsaron Guinea suka bude wuta kan dandazon masu zanga-zangar adawa da Moussa Dadis Camara a Conakry babban birnin kasar inda suka kashe fiye da mutane 150 suka kuma yiwa mata fiye da 100 fyade.

Bachelet babbar jami’ar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, ta koka da yadda gwamnatin kasar a yanzu ta gaza aiwatar da hukunci duk kuwa da kammala bincike kan lamarin a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.