Isa ga babban shafi
Masar

Bana fargabar zanga-zanga al-Sisi

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana cewa, zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa da ake shirin gudanarwa yau Jumma’a ba abin damuwa ba ne.

shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi
shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaban ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Amurka, inda yaje halartan taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74, shugaban cikin murmushi, yace, Masar babbar kasace, kuma yana alfahiri da ‘yan kasar.

A wani yanayi da ba’a saba ba, ‘yan kasar da suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da al-Sisi, a Cairo da wasu manyan biranen kasar, tun a makon jiya, lamarin da ya kai ga kame mutane akalla dubu 2.

‘Yan kasar Masar sun fusata ne, bayan da wani hoton bidiyo da wani dan kasuwar kasar dake gudun hijira ya wallafa a shafukan sada zumun ta, yana mai zargin shugaba al-Sisi da sojojin kasar da sace dukiyar al’umma.

Cikin bidiyon Mohammed Aly yayi ikirarin ginawa shugaba Sisi gidaje har guda biyu ba tare da anbiya shi hakkinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.