MSF ta zargi WHO da takaita raba magungunan Ebola a Congo
Kungiyar Agaji ta ‘Doctors Without Borders’ ta zargi Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da takaita rarraba maganin cutar ebola a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo inda mutane sama da 2,100 suka mutu yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce daya daga cikin matsalolin da su ke fuskanta wajen yaki da cutar ita ce karancin magani, abinda ya sa ake takaita rarraba shi ga tarin mabukata.
Kungiyar ta ce akalla mutane dubu 225 sun karbi allurar rigakafin cutar da kamfanin Merck na kasar Jamus ya samar, amma kuma duk da haka rigakafin ya yi karanci.
Kungiyar ta ce yunkurin ta na samar da maganin wajen hadin gwuiwa da ma’aikatar lafiyar Congo yaci tura, saboda yadda hukumar lafiya ta mamaye aikin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu