Rahotanni sun ce wannan yasa aka jibge jami’an tsaro a Dandalin Tahrir, fitaccen wurin da ya zama dandalin gudanar da zanga zangar shekarar 2011 wadda tayi sanadiyar raba shugaba Hosni Mubarak da kujerar sa.
Hauhawar farashin kayan masarufi da kuma shirin tsuke bakin aljihun gwamnati kasar ta Masar bisa shawarar asusun ba da lamuni na duniya IMF, sun jefa al’ummar kasar cikin halin kuncin rayuwa.
Alkaluma sun bayyana cewar, mutum guda daga cikin 3 na 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.