Isa ga babban shafi
Najeriya

Hare-haren 'yan bindiga ya fi Boko Haram barna a Najeriya- rahoto

Wata kididdiga da kafafen yada labaran Najeriya suka gudanar ta nuna cewa hare-haren ‘yan bindiga da ke ci gaba da addabar sassan kasar sun kashe mutane fiye da yadda kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi tsageru suka yi a cikin watanni 9 da suka gabata.

Yanzu haka dai 'yan bindigar na matsayin na 2 a kungiyoyin ta'addanci da ke kisan kare dangi ga al'ummar Najeriyar.
Yanzu haka dai 'yan bindigar na matsayin na 2 a kungiyoyin ta'addanci da ke kisan kare dangi ga al'ummar Najeriyar. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Kungiyar Boko Haram, wacce ta yi sanadiyyyar mutuwar dubban ‘yan Najeriya a shekaru 10 da suka gabata, ta kasance a kan gaba a cikin kungiyoyi masu ta’asa da salwanta rayuka kafin yanzu.

Kungiyar ta taba kawo karfin da har ta karbe iko da wasu yankuna a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda ta ayyana su a matsayin yankuna da ke karkashin daular Musulunci.

A baya-bayan nan, Boko Haram ta zafafa hare-hare kan soji da fararen hula, inda rahotanni ke nuni da cewa sun mallaki makamai masu nagarta fiye da wadanda suke da su a baya.

Amma nazarin da jaridun kasar suka yi daga watan Janairu zuwa Satumba ya nuna cewa ‘yan bindiga da ke gudanar da ta’asar su a arewacin kasar sun ture Boko Haram zuwa matsayi na biyu a wadanda ke wa ‘yan Najeriya kisan mummuke.

Yayin da Boko Haram ta kashe mutane 370, wato kusan kashi 19 na ‘yan Najeriya 1,950 da kungiyoyi masu aika-aika suka kashe, ‘yan bindiga sun kashe mutanen da suka ninka haka, inda suka kashe 875, kusan kashi 45 na adadin mutanen da suka salwanta; su kuma kungiyoyin asiri, ‘yan fashi da makami, masu satar mutane da sauransu sun kashe mutane 705 a sassan kasar, wato kashi 36 na adadin kenan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.