Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban kasar Tunisiya Ben Ali ya rasu a gudun hijira

Gwamnatin Tunisia ta sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali wanda yake gudun hijira a Saudi Arabia bayan juyin juya halin da ya kawar da shi daga karagar mulki. Ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Tsohon shugaban kasar Tunisiya Zine El Abidine Ben Ali yayin wani ziyara a Faransa
Tsohon shugaban kasar Tunisiya Zine El Abidine Ben Ali yayin wani ziyara a Faransa Handout / AFP
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Tunisia tace tsohon shugaban kasar Zine El Abidine ben Ali ya rasu ne yana da shekaru 83 bayan ya dade yana gudun hijira a Saudi Arabia.

Ben Ali tsohon soja ne da ya karbi mulki a ranar 7 ga watan Nuwambar shekarar 1987 lokacin da ya kifar da gwamnatin shugaban kasa Habib Bourguiba, shugaban da ya jagoranci samun ‘yancin kasar da aka bayyana cewar baya cikin hayyacin sa.

Yan kasar Tunisia sun yaba da juyin mulkin da ba’a zubar da jini ba, abinda ya baiwa Ben Ali damar aiwatar da shirye shiryen sauya alkiblar kasar da ta zama abin misali tsakanin kasashen larabawa da kuma yammacin duniya, duk da sukar da ake masa na kin aiwatar da dimokiradiya.

Tsohon shugaban ya soke dokar shugaban rai da rai da Bourguiba ya ayyana kan sa da kuma sanya wa’adi na uku ga kowanne shugaban kasa, kana da kafa wani asusu na musamman domin marasa galihu da inganta ilimi da kuma ‘yancin mata.

Sai dai an zargi Ben Ali da tirsasawa Yan adawa da kafofin yada labarai da kuma tsawaita mulkin sa.

A shekarar 2010 rasuwar wani matashi ta haifar da zanga zangar da ta tilasta masa barin kasar zuwa Saudi Arabia inda ya samu mafaka kafin rasuwar sa.

An dai haifi shine ranar 3 ga watan Satumban 1936 a garin Hammam-Sousse, yayin da yayi karatun aikin soji a Faransa da Amurka, kafin ya rike mukamin ministan tsaro a shekarar 1985, ministan cikin gida a shekarar 1986 da kuma Firaminista a shekarar 1987.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.