Isa ga babban shafi

Mutane 2 sun mutu a arangama da 'yan sanda a Algeria

Mutane biyu sun rasa rayukansu a kasar Algeria, yayin wata tarzoma cikin dare tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda a yankin Relizane mai tazarar kilomita 300 yamma da birnin Aljas, a dai-dai lokacin da sojin kasar suka umurci jami’an ‘yan sanda da su katse masu zanga-zanga dake wajen babban birnin shiga Aljes.

Wata mata mai zanga-zanga a kasar Algeria
Wata mata mai zanga-zanga a kasar Algeria AFP
Talla

Mai gabatar da kara a kotun Oued-R’hiou kusa da birnin Relizane, yace tarzomar cikin daren da ya hallaka mutanen biyu, ta samu asali ne sakamakon mutuwar wani matashi mai shekaru 15 dake kan babur, bayan da ya ci karo da motar jami’an 'yan sanda.

Lamarin da ya fusata mazauna unguwar, kai ga bore tare da datse babbar titi da duwatsu da kuma kona da tayoyi, matakin da ya kai jam’an tsaro mai da martani, abin da ta kai ga mutuwar mutanen biyu sakamon rauni da suka samu, ko da dai ba a fayyace yanayin raunin da ya kai ga mutuwarsu ba.

Tuni ministan cikin gidan Algeria ya bukaci ofishin shugaban ‘yan sanda da su gudanar da binciki don gano ainihin abin da ya kai ga mutuwar mutanen.

A bangare daya, shugaban dakarun sojin kasar Janar Ahmed Gaid Salah, ya umurci jami’an ‘yan sanda da su katse masu zanga-zanga dake wajen babban birnin kasar shiga Aljes, a kokarin su na gurgunta boren kin jinin gwamnati da ke ci gaba da gudana a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.