Isa ga babban shafi

Kasashe masu tasowa ba za su cimma muradun karni a 2030 ba - Rahoto

Wani rahoto da masana tattalin arziki suka saba fitarwa a duk shekara, yace Najeriya da sauran kasashen dake kudu da Hamada da kuma Karin wasu kasashen masu tasowa ciki harda Indiya, ba za su iya cimma muradun karni, na bunkasar fannin kula da lafiya da kuma Ilimi ba, a shekarar 2030.

Bill Gates, attajirin duniya, kuma shugaban gidauniyar Bill da Melinda Gates mai tallafawa bunkasar Ilimi da samar da lafiya a kasashe masu tasowa.
Bill Gates, attajirin duniya, kuma shugaban gidauniyar Bill da Melinda Gates mai tallafawa bunkasar Ilimi da samar da lafiya a kasashe masu tasowa. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Gidauniyar Bill da Melinda Gates da ta shafe akalla shekaru 20 tana bayarda tallafi kan bunkasa ilimi da lafiya ce ta fitar da rahoton a wannan Talata, inda ta danganta kalulabalen da kasashen ke fuskanta da matsaloli na rashin daidaiton jinsi da kuma tattalin arziki, a mafi akasarin yankunan kasashen masu tasowa da kuma matalauta.

Daya daga cikin muhimman fannonin da rahoton ya yayi tsokaci akai shi ne cimma muradin rage adadin kananan yaran da ke mutuwa musamman ‘yan kasa da shekaru 5, da kuma bunkasa fannin ilimi.

Rahoton na gidauniyar ta Bill da Melinda Gates, yayi karin bayanin cewa, Najeriya da sauran takwarorinta dake yankunan kudu da Hamada, ba wai za su gaza cimma muradun karnin a 2030 bane saboda rashin kokarin samar da tsare-tsaren cimma burin, sai dai za su gaza ne, saboda a halin da ake ciki, akwai yankuna da dama a kasashen da shirin tallafin bai kai gare su ba, saboda rashin daukar matakan fadada shirin akan lokaci.

Ga misali a Najeiya, rahoton ya ce ana sa ran mutanen da ke zaune a Ado Ekiti dake jihar Ekiti, su fi wadanda ke Garki a jihar Jiagawa samun ingantaccen ilimi da kuma kula da lafiya, saboda banbancin adadin kayayyakin kula da lafiyar da kuma yawan makarantu.

Masana tattalin arzikin, sun ce kusan kashi 2 bisa uku na kananan yaran dake kasashe masu tasowa na rayuwa a yankunan da ba za su amfana da ci gaban bunkasar kula da lafiya da kuma samar da ilimi ba, saboda rashin gaggauta fadada matakan cimma muradun karnin, lamarin dake nuni da cewar abu ne mawuyaci, kasashen su cimma muradin rage adadin kananan yara dake mutuwa a matakin kasa da shekaru 5, a shekarar 2030 har zuwa ta 2050.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.