Al'ummar Tunisia na zaben sabon shugaban kasa
Sama da mutane milyan 7 ne suka cancanci kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasa da ake gudanarwar yau lahadi a kasar Turnisia, yayin da aka kafa rumfunan zabe sama da dubu 13 domin bai wa jama'a damar kada kuri'unsu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutane 24 ne ke takara domin maye gurbin shugaba Caid Essebsi wanda ya rasu a cikin watan yulin da ya gabata.
An tsara bude rumfunan zabe da misalin karfe 8 na safe kafin a rufe a 6 na yamma domin bai wa jama’a damar kada kuri’unsu a wannan zabe mai cike da tariki, lura da cewa Tunisia, ita ce kasar larabawa ta farko da aka samu barkewar bore a shekara 2011 sannan aka gudanar da zabe irin na dimokuradiyya a cikinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu