Isa ga babban shafi

Afrika ta kudu ta aike da jakada don ba da hakuri ga kasashen Afrika

Shugaban Kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya aike da jakada na musamman zuwa wasu kasashen Afrika domin kwantar musu da hankali kan hare-haren da ake kai wa baki 'yan kasashen ketare da ke zaune a kasar.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa REUTERS/Rodger Bosch
Talla

Cikin watan jiya kadai, akalla mutane 12 gwamnatin kasar Afrika ta kudun ta tabbatar da mutuwarsu a hare-haren kin jinin bakin da 'yan kasar ke kaiwa kan shagunan baki musamman a birnin Johannesburg inda su ke kwashe musu dukiya.

Tuni dai hare-haren kin jinin bakin suka tilastawa 'yan kasashen Zimbabwe da Mozambique tserewa gida yayinda Najeriya ta kwashe al'ummarta da ke kasar zuwa gida.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Afrika ta kudun ta fitar, ta ce jakadan na musamman Jeff Redabe zai ziyarci kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Senegal da Tanzania da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da kuma Zambia.

Matakin aikewa da jakadan dai na zuwa ne bayan da shugaba Ramaphosa ya nemi gafafar al'umma yayin taron makokin Robert Mugabe a Zimbabwe bayan da al'umma suka fara yi masa kuwwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.