Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 17/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 12/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 17/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 17/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 17/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 17/01 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 17/01 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Sowar kin jini ya katse jawabin shugaban Afrika ta kudu a Zimbabwe

media Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa REUTERS/Philimon Bulawayo

Shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa ya nemi afuwar al’ummar Afrika yayin jawabin da ya gabatar a wajen makokin tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a yau Asabar, bayan da taron jama’a suka rika yi masa kuwwa da kalaman nuna kyama.

Yayin jawabin nuna alhini da Ramaphosa ya fara gabatarwa ihu da sowar nuna kin jininsa ya cika wajen taron makokin yayinda yayi saurin juya jawabin nasa zuwa na neman yafiya da kuma nuna bacin ransa game da hare-haren nuna kin jinin baki da ke faruwa a kasarsa.

Akalla mutane 12 aka kashe cikin watan nan sanadiyyar hare-haren da al’ummar kasar Afrika ta kudu ke kaiwa kan baki ‘yan kasuwa da ma’aikata a birnin Johannesburg da sauran sassan kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa ihu da kalaman nuna kin jinin kan shugaban Ramaphosa sun hana shi kammala jawabansa na makokin Robert Mugabe da ya mutu a cikin makon jiya yana da shekaru 95 a duniya bayan fama da jinya tsawon lokaci.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure