Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/09 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/09 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/09 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/09 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/09 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/09 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/09 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/09 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/09 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/09 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/09 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/09 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/09 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 15/09 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 18/09 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

A cewar lauyansa Mounir Ben Salha, tsohon shugaban Zine El-Abidine Ben Ali ya rasu ne a kasar Saudiya, inda yake gudun hijira.
Ben Ali ya tsere kasar Saudiya ne a shekarar 2011 bayan juyin juya halin kasar Tunisia da ya yadu zuwa kasashen Masar da Libya da kuma Syria.

Afrika

DSS ta koka da yadda labaran karya ke neman hargitsa Najeriya

media Jami'an tsraon farin kaya a Najeriya DSS. guardian.ng

A Najeriya, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta koka da yadda ake samun karuwar labaran karya ta kafar intanet, wanda ka iya ingiza al’umma su tayar da rikici.

Hukumar ta yi wannan bayanin ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun jami’in yada labaran ta, Dr. Peter Afunanya, biyo bayan illar da ta hango kan illar da wannan dabi’ar ka iya haifarwa kasar.

Afunanya ya jaddada jan hankalin da hukumar ta yi tun da farko kan shirin wasu bata garin kungiyoyi na hargitsa tsaron kasar, inda ya ce sun kudiri aniyar amfani da banbance-banbancen siyasa da sauran matsalolin da suka addabi kasar a ciki da wajen ta don bata ta.

A cewar sa, bata garin sun kirkiro labarai masu cike da karairayi don cimma munanan muradinsu na ganin kasar ta barke da rikicin da ke da nasaba da kabilanci da addini wadanda ka iya fitar da kasar daga hayyacinta.

Jami’in ya ce hukumar tsaro ta DSS za ta ci gaba da aiki tukuru don jaddada zaman lafiya tare da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar kasar, sannan ya yi tir da halin rashin kishin kasa da wasu bijirarrun ‘yan kasar ke nunawa, inda yi kashedin cewa doka zata yi halinta a kansu.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure