Isa ga babban shafi
Najeriya-Afrika ta Kudu

'Yan Najeriya 600 sun yi rijistar komawa gida daga Afrika ta Kudu

Mako daya bayan barkewar tarzomar nuna kyamar baki a kasar Afirka ta Kudu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, gwamnatin Najeriya ta ce za ta kwaso ‘yan asalin kasar sama da 600 zuwa gida.

Wasu masu zanga-zangar adawa da hare haren da ake kai wa baki a Afrika ta kudu
Wasu masu zanga-zangar adawa da hare haren da ake kai wa baki a Afrika ta kudu REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Bayan share kwanaki da fara samun kwarya-kwaryan kwanciyar hankali, ko a ranar Lahadin da ta gabata an sake samu wata tarzoma a unguwanni da dama na birnin Johannesburg.

Wannan dai ya tilasta wa jami’an tsaro yin amfani da harsasan roba da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu tarzomar nuna kin jinin ‘yan kasashen Afirka da ke zaune a kasar.

Jakadan Najeriya a birnin Johannesburg Godwin Adamu, ya ce tuni aka tantance mutane kusa da 600 da suka amince a dawo da su gida, kuma za a yi amfani da jiragen kamfanin Air Peace na Najeriya daga ranar Laraba mai zuwa domin fara dawo adadin farko na ‘yan kasar 350 zuwa gida.

Godwin Adamu ya ce za a dawo da sauran ‘yan Najeriya ba tare da bata lokaci ba. A nata bangare gwamnatin Afirka ta ce jami’an tsaro sun cafke akalla mutane 600 da ake zargi da hannu wajen kai wa ‘yan asalin kasashen na Afirka hare-hare, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.