'Yan takarar shugaban kasa za su fara tafka Muhawara a Tunisia
Kwanaki kalilan gabanin fara zaben shugaban kasa a Tunisia yanzu haka ‘yan takarar shugabancin kasar sun shiga wani shirin tafka muhawara tskaninsu ta tsawon kwanaki 3 wadda za ta rika zuwa kai tsaye ga al’ummar kasar.
Wallafawa ranar:
‘Yan takarar 26 dukkaninsu za su yi amfani da damar muhawarar wajen bayyana manufofinsu yayinda za suiya fuskantar tambayoyin kai tsaye daga al’umma baya ga ‘yan jaridu.
Baya ga gidajen Talabijin mallakin gwamnatin kasar da masu zaman kansu wadanda za su watsa shirin muhawarr kai tsaye akwai gidajen radio kusan 20 da za su rika watsa shirin na awa daya da rabi har tsawon kwanaki 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu