Farfesa Abdullahi Zuru kan hukuncin kotun Birtaniya da ya bai wa wani kamfani izinin kwace kadarorin Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:50
Wasu kungiyoyin fararen hula a Najeriya yau sun gudanar da zanga zanga a gaban ofishin Jakadancin Birtaniya da ke birnin Abuja, inda suke bukatar soke hukuncin kotun kasar da ya baiwa wani kamfani umurnin karbe kadarorin gwamnati da suka kai sama da Dala biliyan 9 da rabi, saboda sabawa wata yarjejeniyar kwangilar iskar gas.Kungiyoyin sun bayyana hukuncin kotun a matsayin haramcacce, inda suka bukaci gudanar da bincike kan wadanda ke da hannu wajen badakalar. Dangane da wannan zanga zangar da kuma hukuncin kotun da ya mallakawa kamfanin kadarorin Najeriya, mun tattauna da masanin harkar shari’a da kuma man fetur, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami’ar Abuja, kuma ga tsokacin da yayi akai.