Isa ga babban shafi
Chad

Kotun Chadi ta daure 'yan tawayen Libya 243

Wata kotu a birnin N’Djamena na kasar Chadi ta zartas da hukuncin daurin gidan kaso kan 'yan tawaye 243 da suka kutsa cikin kasar daga Libya a watan Fabrairu da ya gabata.

'Yan tawayen Union of Resistance tare da shugabansu, Timan Erdimi
'Yan tawayen Union of Resistance tare da shugabansu, Timan Erdimi (Photo : Laurent Correau/ RFI)
Talla

Ministan Shari’ar Chadi, Djimet Arabi ya bayyana cewa, jumullar mutane 267 aka kama, inda aka zartas da hukuncin daurin tsawon shekaru 20 kan mutane 12, yayinda sauran mutane 231 aka yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 zuwa 15 bayan an tuhume su da aikata ta'addanci.

A cewar Ministan Shariar, kotun ta kuma yanke wa wasu shugabannin 'yan tawayen kimanin 12 hukuncin zama gidan yari na har abada a bayan idanunsu da suka hada da jagoransu, Timan Erdimi.

Kotun ta samu shugabannin 'yan tawayen da ke rayuwar a kasashen ketare da laifin ta'addanci da kuma shigar da kananan yara cikin ayyukansu.

Tun bayan da ta samu 'yancinta daga kasar Faransa a shekarar 1960,  Chadi ke fama da rikice-rikice.

Kungiyar Union of Resistance ta 'yan tawayen da ke adawa da shugaban kasar, Idriss Deby Itno, ta kafa sansaninta a yankin kudancin saharar Libya, inda take cin karenta babu babbaka.

A watan Fabairun da ya gabata ne, mayakan kungiyar suka kutsa kai cikin arewa maso gabashin Chadi kafin daga bisa  sojin sama na kasar Faransa su fatattake su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.