Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan na bukatar tallafin dala biliyan 8 - Hamdok

Sabon Fira Ministan Sudan, Abdalla Hamdok, ya ce suna bukatar tallafin akalla dala biliyan 8 daga kasashen duniya, domin sake gina tattalin arzikin kasar da ya durkushe, bayan shafe watanni cikin rikicin siyasar da ya kawo karshen mulkin tsohon shugaba Oumar Al-Bashir da kuma shugabancin gwamnatin soji zalla.

Fira ministan Sudan Abdalla Hamdok.
Fira ministan Sudan Abdalla Hamdok. Ebrahim HAMID / AFP
Talla

Fira Ministan ya kuma ce Sudan na bukatar tallafin Karin dala biliyan 2 na dabam, cikin watanni uku masu zuwa, domin farfado da asusun ajiyarta na kasashen ketare.

Ranar Alhamis aka rantsar da Hamdok, tsohon babban jami’in majalisar dinkin duniya, a matsayin shugaban sabuwar gwamnatin Sudan ta hadakar soji da farar hula.

A watan Afrilun da ya gabata, zanga-zangar gama gari kan matsin tattalin arzikin da ya kunshi karancin abinci, man fetur da kuma kudaden ketare, ta tilastawa tsohon shugaban Sudan Oumar Al Bashir rasa kujerarsa, bayan da sojoji suka karbe mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.