Wata majiyar Sojin kasar ta bayyana cewa rikicin yayi sanadin mutuwar sojin kasar 3 yayinda sojin suka yi nasarar hallaka ‘yan bindiga 20.
Ko cikin watan Yunin da ya gabata ma, makamancin rikicin sai da ya hallaka fararen hula 160 baya ga ‘yan bindigar da kuma jami’an tsaron gwamnati.
A ranar 2 ga watan Yulin da ya gabata ne, shugaba Felix Tshisekedi ya yi umarnin fara wani atisayen soji a yankin don kakkabe ‘yan bindigar da ke barazana ga yankunan Djugu da Mahagi mai arzikin ma’adinai.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kawo yanzu mutane dubu dari 3 ne suka tsere daga yankin sanadiyyar ta’azzarar rikicin wanda kan kai ga kisan fararen hula.