Isa ga babban shafi
Rwanda-Uganda-Angola

Rwanda da Uganda sun saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

A ranar laraba 21 ga watan Ogusta 2019 ne a Angola, Shugabannin kasashen Rwanda da Uganda suka sanya hannu kan wata yarjejeniya da zata bada damar kawo karshen zaman tankiyar a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, haka kuma tsohin aminai da ke ci gaba da zagin yi wa junansu liken asiri, kisan siyasa da kuma katsalandan a harkokin cikin gidan kasashensu.

shugaban angola Joao Lourenço kewaye da shuwagabannin kasashen uganda Yoweri Museveni daga hagu da takwaransa na rwandais Paul Kagame a dama bayan  saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar laraba 21 ogusta 2019.
shugaban angola Joao Lourenço kewaye da shuwagabannin kasashen uganda Yoweri Museveni daga hagu da takwaransa na rwandais Paul Kagame a dama bayan saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar laraba 21 ogusta 2019. JOAO DE FATIMA / AFP
Talla

Bayan saka hannu kan yarjejeniyar a Luanda Shuwagabanin kasashen Rwanda Paul Kagame da na Ukanda Yoweri Museveni, sun dau alkawalin mutunta yancin kasashen juna.

Har ila yau mahukumtan biyu, sun dau niyar mutunta tsarin da zai samar da zaman lafiya a cikin kasashensu, tare da kaucewa daukar nauyi, da kuma horar da kungiyoyin dake dauke da makamai wajen rikita tsarin zaman lafiyar kasashen nasu

yarjejeniyar dai an rattaba mata hannu ne a gaban shugabanin kasashen 'Angola, Joao Lourenço, da na jamhuriyar demokradiyar Congo, Felix Tshisekedi, da na dayar Congo, Denis Sassou Nguesso.

Tada jijiyoyin wuya da ake yi tsakanin shugabanin kasashen masu makwabtaka da juna Yuwari Museveni dake kan mulkin Uganda yau da shekaru 33, da Paul Kagame dake kan karaga shekaru 19 da suka gabata, na barazanar tsoma tsama kasshe makwabtansu cikin rikici, tare da haifar da barazana ga tsarin gamayar tattalin arzikin yankin da kuma ci gabansa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.