Isa ga babban shafi

Jiragen Italiya sun ceto tarin 'yanciranin da ke tsibirin Lampedusa

Akalla ‘yancirani 83 jiragen ruwan Italiya suka yi nasarar kwasowa daga tsibirin Lampedusa lokacin da suke ci gaba da iyo a cikin ruwa a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai bayan tsayawar jirgin kungiyar agaji ta Open Arms da ya ceto su amma ya rasa izinin shiga kasar.

Wasu daga cikin 'yanciranin da ke jirgin agaji na Open Arms bayan tsayawar jirginsu a tsibirin Lampedusa
Wasu daga cikin 'yanciranin da ke jirgin agaji na Open Arms bayan tsayawar jirginsu a tsibirin Lampedusa REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Tun a jiya Talata ne wata kotu a kasar ta bai wa gwamnatin Italiya umarnin bayar da damar ceto ‘yan ciranin su kusan 100 bayan da suka shafe kwanaki 19 suna watangaririya a tsakar Teku kafin isowa tsibirin na Lampedusa amma kuma Italiya ta hana su damar ratsawa don shiga nahiyar ta Turai.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan umarnin gwamnatin Italiyan na haramtawa ‘yan ciranin shiga kasar, da dama daga cikinsu sun rika sauka daga jirgin da nufin yin ninkaya don shiga Turai da kansu, matakin da ya janyo cece-kuce musamman tsakankanin kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan adama.

A cewar Oscar Camps wanda ya kafa kungiyar agajin ta open Arms matakin na Italiya babbar nasara ce ga kungiyar ta sa wadda ta yi fadi tashi wajen ganin kasashen na turai musaman italiyan sun karbi ‘yanciranin da aka hanawa isa gabar ruwan Turai.

A nata bangaren ita ma Faransa a jiya ta bakin ministan cikin gidan kasar Christophe Castaner ya ce su na shirin tarbar nasu kason na ‘yanciranin da ke cikin jirgin ruwan jinkan na Ocean Viking, daidai da na cikin jirgin ruwan 'Open Arms, wanda mahukumta paris suka yi alkawalin karbar mutane 40 daga cikinsu

Acikin wata sanrawa a jiya gwamnatin Spain ta ce tun a marecen jiyatalata jirgin ruwan sojanta mai suna Audaz ya fara wata tafiya ta kwanaki uku domin isa tsibirin na Lampedusa, inda zai dau nauyin mutanen da jirgin jinkai na Open Arms ya ceto, domin isar da su a tashar jiragen ruwan Palma de Majorque da ke tsibirin Baléares, a lampadusa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.