Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka ta tallafawa Najeriya da kudaden yaki da cutar HIV Aids

Gwamnatin Amurka ta sanar da matakin sake tallafawa Najeriya da dala miliyan 75 don yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV Aids, dai dai lokacin da masu fama da cutar ke ci gaba da barazanar yadata matukar hukumomi suka gaza samar musu da magungunan rage kaifinta.

Wasu magungunan rage kaifin Cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV Aids.
Wasu magungunan rage kaifin Cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV Aids. Getty Images
Talla

Cikin sanarwar da sashen samar da agajin gaggawa ga cutar ta HIV Aids na fadar shugaban kasar Amurka PEPFAR ya fitar a jiya Talata, ya bayyana cewa kasar za ta karawa Najeriyar agajin dala miliyan 75 don dakushe kaifin cutar.

A cewar jakadan Amurkan a Najeriya Stuart Symington kudaden dala miliyan 75 kari ne kan tallafin kasar ga Najeriya don samar da magungunan rage kaifin cutar ta HIV Aids, dai dai lokacin da Najeriyar ke fuskantar bore daga masu dauke da cutar sakamakon karancin magungunanta.

Mr Stuart Symington ya ce Amurka za ta ci gaba da tallafawa Najeriyar ta hanyar samar mata da kudaden magungunan rage kaifin cutar don rage radadi ga masu dauke da cutar ta HIV Aids mai karya garkuwar jiki.

Matakin na Amurka dai na zuwa a dai dai lokacin da dubunnan al’umma galibi mata da kananan yara da ke dauke dacutar ta HIV Aids ke barazana ga gwamnati Najeriyar sakamakon karanci baya ga tsadar magungunan rage kaifin cutar, inda ko a watanni baya, matan banza da ke dauke da cutar suka sha alwashin ci gaba da yada ta matukar ba a samar da magungunan rage kaifin cutar a saukake ba.

Tallafin na Dala miliyan 75 dai kari ne kan kusan dala biliyan 4 da miliyan 700 da shirin ya kashe a Najeriya cikin shekaru 14 don yaki da cutar ta HIV Aids tun bayan samar da shirin na PEPFAR a shekarar 2003 karkashin shugabancin Gerorge Bush.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.