Isa ga babban shafi
Chad

Shugaban Chadi ya kafa dokar ta baci a gabashin kasar

Shugaban Chadi Idris Deby ya kafa dokar ta baci a wasu yankuna biyu dake gabashin kasar, bayan fuskantar tashin hankalin fadan kabilanci, da yayi sanadin mutuwar gwamman mutane, cikin wannan wata na Agusta.

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno.
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Itno. BRAHIM ADJI / AFP
Talla

Ranar 9 ga watan Agustan da muke ciki, fada ya barke a yankunan Silada Ouaddai, tsakanin makiyaya da manoma, lamarin da yayi sanadin salwantar rayuka 50.

Dokar ta bacin da shugaban na Chadi ya kafa za ta shafe tsawon watanni uku tana aiki, a karkashin sa idon dakarun sojin kasar.

Wata kungiya mai zaman kanta ta ce, rikicin ya samo asali ne a yankin Hamra bayan an  gano gawar wani makiyayi, lamarin da ya haifar da dauki-ba-dadi tsakanin jama'arsa da manoma ‘yan kabilar Ouaddaiens.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.