Isa ga babban shafi
Libya

Amnesty ta koka kan makomar 'yar majalisar Libya da aka sace

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan yadda har yanzu ba a san halin da wata ‘yar majalisar Libya ke ciki ba, wadda ‘yan bindiga suka sace a birnin Benghazi.

Seham Sergewa, ‘yar majalisar Libya da ‘yan bindiga suka sace a birnin Benghazi.
Seham Sergewa, ‘yar majalisar Libya da ‘yan bindiga suka sace a birnin Benghazi. Wikipedia
Talla

Tun a ranar 17 gawatan Yuli yan bindigar suka sace Siham Sergewa, bayan jikkata mijinta, jim kadan bayan zantawar ‘yar majalisar da kafar talabijin ta Al-Hadath dake goyon bayan Janar Khalifa Haftar, mai iko da gabashin kasar ta Libya.

Yayin tattaunawar, yar majalisar da tayi fice wajen sukar dakarun Haftar, ta bukaci gaggauta kawo karshen zubar da jinin ‘yan kasar, da tace yunkurin Janar Haftar na kifar da gwamnatin Libya da kasashen duniya ke marawa baya ya haddasa.

Cikin watan Afrilu Janar Haftar ya kaddamar da farmaki kan dakarun gwamnatin ta Libya, da nufin kifar da ita, inda a yanzu dakarunsa ke kokarin danganewa da hedikwatarta birnin Tripoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.