Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a kammala gina matatar man Dangote karshen 2020

Shahrarren attajirin Najeriya Aliko Dangote, ya ce sai zuwa karshen shekara ta 2020 ne za a kammala aikin gina matatar mai ta farko mallakinsa, wadda ake sa ran bude ta zai sa adadin tataccen mai da ake shiga da shi kasar daga ketare ya ragu.

Aliko Dangote, à Davos, le 22 janvier 2014.
Aliko Dangote, à Davos, le 22 janvier 2014. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Daya daga cikin manyan daraktocin kamfanin na Dangote, Mista Devakumar Edwin ya ce bayan kammala aikin a karshen shekara ta 2020, matatar da ke birnin Lagos za ta iya tace mai da adadinsa zai kai ganga dubu 650 a kowace rana ta Allah.

Duk da cewa Najeriya na da dimbin arzikin man fetur, to sai dai ya zama dole sai kasar ta fitar da gurbataccen mai zuwa ketare, wanda ake tacewa sannan a sake dawo da shi, abin da ke haddasa asarar kudade masu tarin yawa ga kasar.

A makon da ya gabata,shugaban kamfanin mallakin gwamnatin Najeriya NNPC Kyare Kolo Mele, ya ce za su yi aiki kafada da kafada Dangote, domin samar da wadataccen mai a Najeriya har ma da fitar da shi zuwa sauran kasahe na ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.