Mutanen wadanda matasa ne, akasari ‘yan Sudan, da suka baro Libya a daren Asabar a wani kwale kwalen balam – balam, sun yi ta tafi da sowa yayin da suka hango jirgin tafe.
Aikin ceton na wannan Lahadi shine na uku a cikin kwanaki ‘yan kwanaki
Jirgin wanda mallakan hadin gwiwa ne tsakanin SOS Mediterranean da Medecins Sans Frontieres, ko Doctors without Borders, ya yi sintirin tekun ne har na mil 50 zuwa tekun Tripoli.
Shuagaban aikin ceto na kungiyar SOS Mediterranean, Nicholas Romaniuk ya shaida wa kamfanin dillancin labarana Faransa cewa, su kadai ne ke yankin saboda jami’en tsaron Libya ba sa kai dauki ko da an bukaci haka daga garesu.
Ya kara da cewa kyaun yanayi zai karfafa wa ‘yan ciranin shiga tekun daga Libya, bugu da kari, hutun da aka fara na babbar Sallah a Lahadin nan, wadda sanadinsa babu jami’en tsaro masu sintiri zai kara wa bakin hauren karsashin barin gari ta teku.
A ranar Juma’a, kungiyar ta ceto wasu daga yammacin Afirka akasari daga Senegal da Ivory Coast wadanda suka shiga Libya da zummar neman aiki, amma rikici ya rutsa da su.