Isa ga babban shafi

'Yan Zimbabwe miliyan 5 na fama da matsananciyar yunwa- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shirin neman tallafin dala miliyan 331 don kai daukin gaggawa ga al’ummar kasar Zimbabwe fiye da miliyan 5 da ke fuskantar tsananin yunwa.

Wasu al'ummar Zimbabwe da yunwa ta galabaita
Wasu al'ummar Zimbabwe da yunwa ta galabaita REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Shirin wanda hukumar kula da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar a jiya, ta ce zai agazawa kashi 1 bisa ukun al’ummar Zimbabwe da ke fuskantar matsananciyar yunwar tsawon lokaci sanadiyyar farin da kasar ke fama da shi dama mashassharar da tattalin arzikinta ke fuskanta.

A cewar Majalisar, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, za a iya fuskantar karin mutane miliyan 5 da yunwar za ta shafa a kasar ta Zimbabwe cikin shekara mai zuwa sakamakon yadda farashin abinci ke kara yin tashin gwauron zabi baya ga karancin abincin sanadiyyar fari.

Hukumar samar da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yanzu haka mutane miliyan 2 sa dubu dari biyar basa iya samun abincin da za su ci kowacce rana a kasar ta Zimbabwe yayinda wasu Miliyan biyar ke iya samun 1 bisa ukun abincin da suke bukata don samun wadatacciyar lafiya.

Da ya ke jawabi lokacin kaddamar da gidauniyar neman tallafin daraktan hukumar samar da Abincin na Majalisar Dinkin Duniya David Beasley ya ce akwai bukatar kai daukin gaggawa kasar ta Zimbabwe la’akari da yadda yunwa ke ci gaba da tagayyara jama’a ciki har da kananan yara.

Majalisar ta bbayyana cewa, baya ga matsalar tattalin arziki da kuma Farin da ya dabaibaye Zimbabwe ambaliyar ruwa da guguwar Idai sun taka muhimmiyar rawa wajen sake tagayyara kasar, ta hanyar jefa mutane akalla dubu dari 570 cikin matsanancin talauci da rashin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.