Isa ga babban shafi
Libya

Dakarun Haftar sun kai kazamin farmaki a kudancin Libya

Akalla mutane 42 aka halaka tare da jikkata wasu da dama, yayin farmakin da jiragen yaki suka kai kan garin Morzuk da ke kudancin kasar Libya.

Wasu daga cikin sojoji masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar mai iko ga yankin gabashin kasar Libya.
Wasu daga cikin sojoji masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar mai iko ga yankin gabashin kasar Libya. REUTERS/Stringer
Talla

Tuni dai gwamnatin Libya da kasashen duniya ke marawa baya, suka dora alhakin harin kan rundunar sojojin da ke yiwa Janar Khalifa Haftar biyaya mai iko da gabashin kasar.

Yayin maida martani dakarun na Janar Haftar sun tabbatar da kai farmakin, sai dai sun musanta cewa sun kai harin ne kan fararen hula, inda suka halaka mutane 42, tare da jikkata wasu 60, 30 daga ciki kuma sun halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Tun a watan Afrilun wannan shekara Janar Haftar ya kaddamar da yaki kan gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan kasashen duniya, da nufin hambarar da ita, kuma zuwa yanzu ya kwace yankunan kudancin kasar ta Libya da dama inda yake kokarin kutsawa birnin Tripoli.

Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa, sabon fadan da ya barke tsakanin sojin gwamnatin Libya da dakarun Khalifa Haftar, ya tilastawa mutane sama da dubu 75,000 tserewa daga muhallansu, yayinda wasu sama da dubu 1 da 500 suka halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.