Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan: Masu fafutuka sun bukaci fita sabuwar zanga-zanga

Kungiyar dake jagorancin masu zanga zangar Sudan ta kira zanga zangar kasa baki daya domin nuna bacin ranta kan abinda ta kira kisan kiyashin da aka yiwa mutane biyar cikinsu harda dalibai guda 4.

Masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Masu zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar Sudan. REUTERS/Umit Bektas
Talla

Kungiyar ta kwararrun Sudan da ta kaddamar da zanga zangar da ta kifar da mulkin shugaba Omar Hassan al Bashir ta kira sabuwar zanga zangar ta gama gari, saboda bukatar ganin an kama jami’an tsaron da suka aikata kisan gillar da niyar hukunta su.

Wannan ya biyo bayan kashe mutane biyar da akayi jiya, cikin su harda da dalibai guda 4, a daidai lokacin da ake tababar rahotan binciken kisan gillar da aka yiwa masu zanga zanga sama da 100 a watan Yuni, wanda ya wanke shugabannin sojin kasar.

Yau ne aka shirya shugabannin masu zanga zangar da sojojin dake mulkin kasar zasu sake komawa teburin tattaunawa domin kamala shirin kafa gwamnatin hadin kan kasar, amma ya zuwa yanzu babu tabbacin ko taron na yau zai gudana, ganin tashin hankalin da aka samu jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.