Isa ga babban shafi
Afrika

An ceto wasu bakin haure a Morocco

Sojan ruwan Morocco sun yi nasarar ceto bakin haure 242 da akasarin su yan kudancin Sahara ne dake kokarin tsallakawa zuwa Turai a dai-dai lokacin da kwalekwalon dake dauke da su ya nemi nutsewa.

Wasu daga cikin bakin haure da ke neman zuwa Turai ta tekun Libya
Wasu daga cikin bakin haure da ke neman zuwa Turai ta tekun Libya Taha JAWASHI / AFP
Talla

Daga cikin bakin haure da aka ceto an gano mata 50,da kananan yara 12 da suka fito da yankinkudancin Sahara kama daga cikin daren Alhamis zuwa juma’a.

Kasar Morocco na daga cikin kasashen da suka tsananta dokkokin su na yaki da kwarrarar bakin haure, alkaluma na nuna cewa kasar ta kama bakin haure dubu 89 da suka nemi tsallakawa zuwa Turai a shekara ta 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.