Isa ga babban shafi
Sudan

An kame masu yunkurin hambarar da gwamnatin Soji a Sudan

Shugabannin Sojin da ke mulkin Sudan sun sanar da kama wani babban Janar na sojin kasar da wasu jami’ai da dama da ake zargi da yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba.

Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan Abdulrahman, shugaban gwamnatin Soji a Sudan
Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan Abdulrahman, shugaban gwamnatin Soji a Sudan Sudan TV / AFP
Talla

Sanarwar sojin ta ce cikin wadanda aka kama harda Janar Hashim Abdel Mottalib, shugaban Hafsan Hafsoshin sojin da kuma wasu jami’ai da ke hukumar leken asiri ta kasar.

Sanarwar ta ce an kuma kama wasu shugabannin kungiyar Islama da na Jam’iyyar NCP ta tsohon shugaban kasa Omar Hassan al Bashir wadanda suma ke da hannu dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin.

Bayan tsanantar zanga-zangar adawa da gwamnati biyo bayan tsadar rayuwa a kasar ta Sudan, Sojin kasar suka hambarar da gwamnatin shugaba Omar Hassan al Bashir tare da daure shi a gidan yari biya bayan zarge-zarge.

Yanzu haka dai Sojin za su gudanar da mulkin kasa da shekara biyu don daidaita al'amura a kasar kafin mika ragamar jagoranci ga fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.