Cikin sanarwar kungiyar ta ACF mai rajin yaki da yunwa a yankunan da rikici ya daidaita, ta ce yayin farmakin mayakan na Boko Haram sun hallaka direba guda da ke tuka motar da ke dauke da kayakin agajin, yayinda mutane 6 cikin har da jami’in agaji guda suka bace.
Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta hannun babban jami’in da ke kula da ayyukan jinkai Edward Kallon ta aike da sakon ganin hukumomin Najeriyar sun yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin mutanen 6 sun dawo da lafiyarsu.